✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An lakaɗa wa Ɗan Bilki Kwamanda duka saboda sukar Gwamnan Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta ba da umarnin gudanar da bincike kan dukan da aka yi wa Dan Bilki.

Ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya sha dukan tsiya kan zargin sukar Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani.

Cikin wani hoton bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta, an ga yadda wasu da ba iya gane fuskokinsu ba suka riƙa yi wa Ɗan Bilki ruwan bulalai yana dature da ankwa a hannu.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, mutanen sun fara neman ya gabatar da kansa sannan suka biyo da tambayoyi kan dalilin da yake caccakar Gwamna Uba Sani alhahi shi ba ɗan asalin Jihar Kaduna ba ne.

Daga bisani kuma suka riƙa tsiyaya masa bulalai duk da ya riƙa ba su hanzarin cewa yana fama da rashin lafiya ta hawan jini da ciwon suga amma suka yi biris da shi.

A cikin wani bidiyon na daban da ya biyo bayan wannan, Aminiya ta ga Ɗan Bilki a tuɓe babu riga a jikinsa duk bayansa zuwa ƙeyarsa sun yi ruɗu-ruɗu na alamar wanda ya sha tsimangiya.

A wannan bidiyon, Ɗan Bilki ya bayyana cewa ’yan sanda ne suka yi masa wannan wulaƙanci bisa umarnin Gwamnan na Kaduna.

Ya ce “Gwamna Uba Sani ne ya turo su suka zane ni. Zan iya gane fuskokin wasu daga cikinsu da wurin da suka samo ankwar da suka ɗaure ni da ita.

“Dubi yadda jikina ya yi ruɗu-ruɗu. ’Yan sanda ne suka yi min haka kuma Uba Sani ne ya ba su umarni.

“Har da cewa za su kashe ni su jefa gawata cikin ruwa.

“Sun riƙa ɗaukata a bidiyo yayin da suke zuba min bulalai. An wulaƙanta ni matuƙa,” a cewar Ɗan Bilki.

Tuni dai Gwamnatin Kaduna cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin jihar, Muhammad Lawal Shehu ya fitar ta nesanta kanta daga wannan zargi da Ɗan Bilki ya yi.

A cikin sanarwar, Gwamnatin ta Kaduna ta ce ba za ta taɓa goyon bayan irin wannan wulaƙanci da aka yi wa Ɗan Bilki ko waninsa ba, saboda haka ta ba da umarnin a gudanar da bincike domin gano masu hannu a wannan aika-aikar.

Ɗan Bilki Kwamanda wanda ɗan jam’iyyar APC ne ya shahara wajen kwance wa ’yan siyasa zane a kasuwa musamman a hirarrakinsa da gidajen rediyo.