✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwaso ’yan Najeriya 542 da suka makale a Dubai

An haramta bai wa ’yan Najerya bizar zuwa har sai an samu daidaito a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.

Gwamnatin Tarayya ta nasarar ’yan Najeriya 542 da suka makale a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Da safiyar Lahadi suka sauka Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Tawagar Gwamnatin Tarayya, karkarkashin jagorancin Hukumar ba da Agajin Gaggawa (NEMA) da sauransu ce ta tarbe su a filin jirgin.

Bayan isowarsu, jami’ai sun tantance lafiyarsu da sauran bayanansu, sannan hukumar NEMA ta tallafa musu da ’yan kayayyakin masarufi.

Tun farko da yake jawabi, Darakta-Janar na hukumar NEMA, Mustapha Habib Ahmed, ya yi kira ga wadanda aka kwason da su koyi darasi daga abin da ya farau da su, sannan su zamo ’yan kasa masu bin doka da oda da kare martabar kasa.

A nata bangaren, Jakadiyar Najeriya a Dubai, Atinuke Taibat Mohammed, wadda ta yi wa ’yan Najeriyar rakiya zuwa gida, ta yaba da kokarin gwamnatin wajen jigilar su zuwa gida.

Idan ba a manta ba, a karshen makon da ya gabata hukumomin Dubai suka ba da sanarwar dakatar da bai wa ’yan Najerya biza har sai an samu daidaito a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.