Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta amince da ta ci gaba da bai wa ’yan Najeriya biza.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
- Ranar Matasa Masu Sana’a: Yadda matasa 136 suka baje-kolin fikirarsu a Kano
- Kotu ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, a baya ya ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta kusa dawo da bai wa matafiyan Najeriya biza.
Keyamo, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu da shugaban UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan, sun cimma yarjejeniya yayin ziyarar da Tinubu ya kai Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a watan Satumban 2023.
Ya ce akwai matakai da dama da gwamnatocin ƙasashen biyu suka ɗauka kafin ɗage haramcin da aka ƙaƙaba wa matafiyan Najeriya.
“Bayan wannan muhimmin taro, shugaba Tinubu ya sauƙaƙa mana al’amura. Mun bi sahun lamarin a matsayinmu na ministocinsa kuma muka warware komai,” in ji Keyamo.
Ɗage haramcin zai sauƙaƙa wa ’yan Najeriya da ke tafiye-tafiye zuwa UAE, kuma zai inganta dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.