✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwaso karin ‘yan Najeriya 418 da suka makale a Saudiyya

Karin wasu ‘yan Najeriya 418 da suka makale a kasar Saudiyya sun sauka a birnin Abuja. Hukumar NIDCOM mai kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare…

Karin wasu ‘yan Najeriya 418 da suka makale a kasar Saudiyya sun sauka a birnin Abuja.

Hukumar NIDCOM mai kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare ce ta sanar da hakan cikin wani sako da ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Twitter.

NIDCOM ta ce jirgin Saudi Air ne ya kwaso sawu na uku na ‘yan Najeriya yayin da suka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja.

Sanarwar ta ce za a killace su a sansanin Alhazai na tsawon kwanaki uku kacal gabanin a bari su tafi gidajensu.

Kazalika, za’a rarraba wa kowanensu naira dubu ashirin domin su yi kudin komawa gidajensu kamar yadda Ambasada Bolaji Akinremi, Daraktan sashen shari’a na Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ya sanar.

Kawo yanzu, ’yan Najeriya 1,071 ne aka dawo da su daga kasar Saudiya cikin kwanaki ukun da suka gabata.