✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya a asibiti  

Hakan n zuwa ne ’yan watanni bayan an yi masa aiki a zuciyarsa

An sake kwantar da Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul’Aziz domin duba lafiyarsa a birnin Jiddah, ’yan watanni bayan an yi masa aiki a zuciyarsa.

Wata sanarwa ta Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya ta ce an kwantar da Sarkin mai shekara 86 a Asibitin Kwararru na Sarki Faisal da ke birnin Jiddah na kasar.

Sai dai kafar yada labaran bai bayyana abun da ke damun Sarkin ba da kuma nau’in gwaje-gwajen da za a yi masa.

“Muna addu’ar Allah ya ba wa mai kula da Masallatan Harami na Makka da Madina lafiya,” kamar yadda sanarwar da fadar Sarkin ta fitar.

Ko a farkon wannan shekarar dai sai da aka kwantar da Sarki Salman a asibiti a babban birnin Riyadh domin canja masa wani abu a zuciyarsa.

Bugu da kari, a shekarar 2020 ma an yi masa aiki a mafitsarar shi bayan an jima ana ta rade-radi kan lafiyarsa.

Salman dai ya dare kan karagar sarautar kasar ne tun shekarar 2015, kuma tun a lokacin ya nada dan shi, Muhammad Bin Salman a matsayin Yarima mai jiran gado.

Galibi dai Yariman ne ke gudanar da yawancin harkokin mulkin kasar a madadin mahaifin na shi.

%d bloggers like this: