✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwantar da Osinbajo a asibiti

Osinbajo ya ji rauni yayin buga wasan squash.

Za a yi wa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo tiyata a kafarsa bayan kwantar da shi a asibiti a Asabar din nan.

Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasar, Laole Akande ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Mista Akande ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasar ya ji raunin ne yayin wani wasan motsa jiki da a turance ake kira squash.

Ya kara da cewa, nan gaba kadan ne likitocinsa za su yi bayanin halin da yake ciki.