✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwantar da Muhammad Ali a asibiti

An sake kwantar da zakaran damben boding na duniya Muhammad Ali a asibiti bayan ya kamu da ciwon sanyi na nimoniya (Pneumonia).A yanzu Muhammad Ali…

An sake kwantar da zakaran damben boding na duniya Muhammad Ali a asibiti bayan ya kamu da ciwon sanyi na nimoniya (Pneumonia).
A yanzu Muhammad Ali yana da kimanin shekara 72 a duniya.  Baya ga cutar nimoniya, tun farko dan damben yana da lalurar cutar kakkarwar jiki (Parkison) al’amarin da ya sa ba a iya yin magana a mafi yawan lokuta ganin yadda bakinsa ke rawa da hannayensa da kuma kafafuwansa. Tarihi ya nuna dam damben ya kamu da cutar ta kakkarwa ce a lokacin da yake wasan damben boding inda aka rika narkarsa a kai da hakan ya sa cutar ta shafi kwakwalwarsa.
Sai dai kawo yanzu hukumomin asibitin sun bayar da sanarwar Muhammad Ali yana samun sauki kuma da alama an kusa sallamarsa.
A shekarar 1984 ce Muhammad Ali ya kamu da cutar kakkarwar jiki watau shekara uku kacal bayan ya yi ritaya daga wasan damben boding. Rahoton ya ce saboda irin naushin da ya rika samu a ka a yayin da yake wasan damben boding ce ta sa Muhammad Ali ya kamu da cutar ta kakkarwa al’amarin da ya sa cutar ta rika kamari a jikinsa bayan ta shafi kwakwalwa.  An ce tun bayan da ya yi ritaya cutar ta cigaba da karuwa al’amarin da ya sa aka rika kwantar da shi a asibiti a lokuta da dama inda Likitoci ke duba lafiyarsa ana ba shi magani kafin ya samu sauki.  
Likitoci sun tabbatar da cewa cutar kakkarwar jiki (Parkison) cuta ce da ke iya kashe mai fama da ita a kowane lokaci saboda cuta ce da take shafar jijiyoyin jikin dan Adam da hakan ya sa ba a iya magana ko tsayuwa ko aiki da hannuwa a mafi yawan lokuta sai dai jiki ya rika kakkarwa.  
An ce kawo yanzu Muhammad Ali ba ya iya yin magana al’amarin da ya sa ya daina halartar tarurrukan da aka gayyace shi sai dai kawai ya zauna a gida ya kalla a akwatin talbijin.  Hakan ta sa rabon da aka ga Muhammad Ali a bainar jama’a tun cikin watan Fabrairun wannan shekara a lokacin da ya halarci wani taro da Shugaban Amurka Barack Obama ya shirya a Amurka.  An ce ko a wajen taron ma da kyar aka mayar da Ali gida bayan cutar ta sarke shi kuma nan da nan aka garzaya da shi asibiti kafin a kai shi gida bayan an sallame shi.
 Sai ga shi a ranar Litinin da ta wuce ne aka sake kwantar da Ali a asibiti bayan ya  kuma da cutar sanyi ta nimoniya (Pneumonia).
  Ya zuwa wannan lokaci dai abubuwa uku ne suka damun shararren dan damben boding Muhammad Ali.  Na farko shi ne tsufa, don yanzu yana da shekara 72 a duniya sannan ga cutar kakkarwar jiki yayin da ta sanyi nimoniya ta sake kama shi.
A tarihin damben boding ba a taba samun dan damben da ya kama kafar Muhammad Ali ba tun bayan da ya yi ritaya a shekarar 1981.
An sha rade-radin ya mutu ganin yadda akan dade ba a ji duriyarsa a bainar jama’a ba.