An kwantar da wani magidanci a asibiti bayan matarsa ta yi masa dukan kawo wuka har sai da ya fadi ranga-ranga, bai san inda yake ba.
Magidancin mai shekara 56 ya bayyana wa kotu yadda matarsa tasa take yawan lakada masa duka a kan abin da bai taka kara ya karya ba.
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda NYSC Ta Canza Rayuwata’
- Ba mu yarda da tsarin raba shugabancin Majalisun Tarayya ba —Akeredolu
Mista Edwin Ogwu ya bayyana wa kotun majistare da ke yankin Ogba a Jihar Legas, cewa abin ya kai makura a baya-bayan na, inda matar ta yi masa duka, har sai da ya fadi magashiyyan, aka kwashe shi zuwa asibiti rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Dan sanda mai gabatar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya bayyana wa kotun cewa ma’auratan sun samu sabani ne da ya kai ga matar ta yi wa mijin nata duka kawo wuka.
Sai dai matar, wadda aka gurfanar, ta musanta zargin da ake mata da cin zarafi da yin raunin ga mijin nata.
A kan haka ne mai gabatar da kara ya nemi kotun ta sanya ranar sauraron shari’ar, kuma alkali Misis E. Kubenije ta sanya ranar 6 ga watan Yuni, 2023 domin ci gaba da shari’a.
Kotu ta kuma bayar da belin matar a kan Naira dubu 100 sannan ta kawo mutum biyu da za su tsaya mata.