✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwantar da Fafaroma a Asibiti

Za a yi masa tiyata a wani bangare na babban hanjinsa.

An kwantar da Fafaroma Francis a Asibiti a wani mataki na shirin yi masa tiyata a cikinsa da zummar magance wata matsala da ta shafi ’ya’yan hanjinsa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Vatican, Matteo Bruni, ya ce zuwa gaba za su yi karin bayani bayan an kammala tiyatar da za a yi masa a Asibitin Jami’ar Gemelli da ke Rome.

Sanarwar ta ce Fafaroma na son a magance masa matsalar da ta shafi wani bangare na babban hanjinsa.

Rahotanni sun ce gabanin kwantar da shi, Fafaroma ya gabatar da jawabai ga dmbin mabiya da suka ziyarci Dandalin St Peter da safiyar Lahadi.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, wannan shi ne karon farko da aka kwantar da shi a asibiti tun bayan zabensa a shekarar 2013.