✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kwace bindigogi 5 a hannun wadanda ake zargi da kai hare-hare a Osun

’Yan sanda a Jihar Osun sun ce, sun cafke mutum 10 da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai a wasu tashar motoci…

’Yan sanda a Jihar Osun sun ce sun cafke mutum 10 da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai a wasu tashoshin motoci a sassan jihar.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin, mai magana da yawun Rundunar a jihar, SP Yemisi Opalola, ya ce sun kwace bindigogi da alburusai da adduna daga hannun wadanda ake zargin.

Rundunar ta ce, tana sane da hatsaniyar da ta faru a tsakanin mambobin kungiyar direbobi ta NURTW a safiyar Litinin a jihar.

Sanarwar ta ce tun farko Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da sauran masu ruwa da tsaki sun gana da shugabannin kungiyar ta NURTW don kashe wutar rikicin da ta taso.

Rundunar ta ce ta yi mamakin yadda mambobin NURTW suka kai hare-hare a wasu sassan jihar inda suka lalata ofisoshi da ji wa wasu rauni, ciki har da jami’an ’yan sanda.

(NAN)