✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kuɓutar da ’yar shekara 4 daga hannun mai garkuwa da mutane a Kano

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kuɓutar da wata ƙaramar yarinya mai shekara huɗu daga hannun wani mai garkuwa da mutane. Mai magana…

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kuɓutar da wata ƙaramar yarinya mai shekara huɗu daga hannun wani mai garkuwa da mutane.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kiyawa wanda ya wallafa bidiyon matashin — Saifullahi Abba mai shekaru 23 —  yana amsa tambayoyi, ya bayyana cewa tun a ranar Talata ce jami’an ’yan sanda suka kama shi bisa zargin garkuwa da yarinyar.

Ya bayyana cewa kamen na zuwa ne bayan mahaifin yarinyar mai suna Zilkiflu Abdullahi da ke zaune a ƙauyen Dakatsalle na Ƙaramar Hukumar Bebeji ya kai wa ’yan sanda ƙorafin sace ’yar tasa mai suna Nabila a ranar 22 ga watan Nuwamban da muke ciki.

“Kwana guda bayan haka kuma sai wani mutum ya kira shi tare da iƙirarin sace ’yar tasa yana mai neman naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa,” a cewar Kiyawa.

Kiyawa ya ƙara da cewa, sun kama wanda ake zargi da sace yarinyar — wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Wudil ne — a ƙauyen Luran da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu.

“Wanda ake zargin ya amince da laifin da aka tuhume shi, sannan ya jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa inda ya ɓoye yarinyar a ƙauyen na Luran, inda nan take aka kuɓutar da ita.”

Sanarwar ta ambato Kwamishinan ’yan sandan Kano yana nanata cewa za su ci gaba aiki ba dare ba rana domin kakkaɓe ayyukan miyagu a jihar.

Kazalika, ya gargaɗi mazauna da su ci gaba da sa ido kan duk wani motsi da ke faruwa tare da neman su ƙara azama wajen bai wa ’yan sanda haɗin kai.