Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Bauchi, Alhaji Abdulrazaq Nuhu Zaki, ya ce jami’an tsaro da ’yan banga sun kubutar da mutum 69 da aka yi garkuwa da su, a wani samame a sansanin ’yan bindigar a dajin.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Bauchi yayin da yake amsa tambayoyi daga ’yan jarida kan farmakin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kananan hukumomin Toro da Alkaleri da Tafawa Balewa da Ningi a jihar.
- Masu garkuwa da Kwamishinan Nasarawa na bukatar N100m
- ’Yan banga sun harbe mace mai garkuwa da mutane, sun kama wasu wasu 12
A cewarsa, “Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya jagoranci jami’an da kansa.
“Ya ziyarci yankunan da lamarin ya shafa, ya jajanta wa jama’a tare da karfafa musu gwiwa da su bijire wa masu garkuwa da mutane.
“Hakazalika, ya kara wa shugaban karamar hukumar da ’yan banga da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kwarin gwiwa.
“Mun tattara kanmu, jami’an tsaro da ’yan banga, muka kutsa cikin dajin ba tare da tsoro ba, muka fuskanci ’yan bindigar.
“Sai suka gudu, amma mutanenmu suka ci gaba da bin su.
“Shugabannin kananan hukumomin sun kawo mana rahoton cewa adadin mutanen da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su sun kai 69 kuma an kubutar da su duka.
“Wadanda aka yi garkuwa da su an ajiye da yawa daga cikinsu a Bauchi.
“Bayan kubutar da su muka bar su su koma gidajensu,” in ji shi.