’Yan sintiri sun kubutar da mutane 62 daga hannun masu garkuwa da mutane a wani daji da ke kan iyakar jihohin Taraba da Binuwai.
Wadanda aka kubutar din ’yan asalin guruwan Takum da Wukari ne a Jahar Taraba kuma sun kwashe watanni a hannun masu garkuwar.
- COVID-19 ta kashe ’yan majalisa 32 a kasar Kwango
- Real Madrid ta sake daukar Ancelotti a matsayin sabon Koci
Rahotanni sun ce ana kyautata zaton cewa ’yan bindigar yaran kasurgumin dan bindigar nan ne mai suna Gana, wanda aka kashe a Jihar Biniwai.
Wani mazaunin garin Takum mai suna Mallam Maiwada ya shaidawa wakilin Aminiya cewa sai da aka biya kudin fansa kan wasu daga cikin wadanda aka kubutar din amma masu garkuwar suka suka ki sakinsu.
A cewarsa, ’yan bindinga sun kuma sace fasinjoji a cikin motocin haya kirar Sharon da Homa wadanda suma aka kubutar da su ko da yake ba a sami motocin nasu ba.
Kazalika, shima wani mazaunin garin Wukari mai suna Mallam Idi Ruwaya,ya bayyanawa Wakilin Aminiya cewa fasinjoji bakwai wadanda aka sace a cikin motar Sharon suma an kubutar da su kuma tuni suka koma gidajensu a garin Wukari.
Binciken Aminiya ya gano cewa akasarin wadanda aka kubutar din an sace su ne akan hanyar Takum zuwa Wukari da kuma kan hanyar Takum zuwa Wukari da hanyar Takum zuwa Kashinbila.
Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Taraba, DSP David Misal ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ba su sami rahotan kubutar da mutanen su 62 daga hannun masu garkuwa da mutane ba.