✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kubutar da mutum 16 daga hannun masu garkuwa

’Yan Sandan sun kubutar da mutum 16 da aka yi garkuwa da su a Ogor, Karamar hukumar Ughelli ta Kudu a Jihar Delta. Kakakin Rundunar…

Yan Sandan sun kubutar da mutum 16 da aka yi garkuwa da su a Ogor, Karamar hukumar Ughelli ta Kudu a Jihar Delta.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa an kubutar da mutanan da aka yi garkuwar da su a ranar Laraba.

“Da misalin karfe 9.37 na dare ranar Laraba 3, ga watan Maris, 2021, an kira mu cewa an yi garkuwa da ma’aikata 16 na wani mai otal, Mista Zion Onofighe bayan ‘yan bindiga sun kai hari otal din da ke Ogor, Ughelli.

“Mun baza jami’anmu don kai sumame kuma daga bisani suka yi nasarar cafke masu garkuwar bayan da suka ji karar bindiga.

“An kubutar da su an kuma karbe wata mota kirar Toyota Highlander Jeep daga hannun masu garkuwar a yayin artabun,’’ inji Edafe.