Mummunan karyewar darajar Naira ya shafi daliban Najeriya da ke karatu a Jami’ar Teesside da ke kasar Birtaniya.
Kawo yanzu dai Jami’ar Teesside ta kado keyar daliban da suka kasa biyan kudin makaranta.
Wasu daga cikin daliban sun shaida wa BBC cewa sun ji takaicin abin da jami’ar ta yi na rashin kulawa da matsalolinsu.
Duk da koke-koke da kokarin da daliban suka yi na yin shawarwari da tsare-tsare na biyan kudin, jami’ar ta kaddamar da tsauraran ka’idojin biza, lamarin da ya sa aka rufe asusun daliban aka kuma soke bizarsu.
- Shaida ya fadi ya mutu ana shari’a cikin kotu
- NAJERIYA A YAU: Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC?
Jami’ar ta ce rashin biyan kuɗin makarantar ya saba wa sharuddan bizar da aka ba wa daliban.
Daliban da abin ya shafa sun ce suna cikin tsananin damuwa sakamakon ƙin taimaka musu da jami’ar ta yi; duk da iƙirarin jami’ar ta yi na bayar da taimako ga wasu daga cikinsu.