Rundunar ’Yan Sandan Najeriya a ranar Alhamis ta sanar da korar jami’anta da ke gadin fitaccen mawakin nan na jam’iyyar APC, Dauda Kahutu (Rarara), daga bakin aiki.
An dauke matakin a kan jami’an ne bayan an same su da laifin harbi da harsashi ba bisa ka’ida ba.
Kakakin rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya sanar da korar a wata sanarwa a Abuja da yammacin Alhamis.
Ya ce rundunar ta yanke wa jami’an nata uku hukuncin ne bayan sun fuskanci tuhuma daga wani kwamiti da rundunar ta kafa don binciken zarge-zargen da ake musu.
Bayanai sun nuna tun asali ’yan sandan an debo su ne daga sashen SPU na rundunar da ke Kano, bayan mawakin ya dauki ‘hayarsu’ daga rundunar don su rika ba shi kariya a karkashin wani sabon tsari.
Sai dai a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na intanet, an ga biyu daga cikin jami’an na harbi a sama, lokacin da Rarara ke kokarin shiga motarsa kirar SUV bayan ya kammala rabon kayan tallafin azumi a garinsa na Kahutu da ke Jihar Katsina.
Daga bisani an gano ’yan sandan da suka hada da Insfekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da kuma Sajan Isah Danladi, inda aka kama su sannan aka tisa keyarsu zuwa hedkwatar rundunar ta kasa bisa zargin yin harbi ba bisa ka’ida ba.
A cewar Kakakin ’yan sandan na kasa, yin harbe-harben da jami’an suka yi da bindigarsu ta aiki ya saba da tsarin rundunar.