✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori ’yan sanda 3 daga aiki saboda rashin da’a

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kori jami’anta uku daga makarantar horar da ’yan sanda ta Ogida da ke Jihar Edo, saboda rashin da’a. Kwamandan makarantar,…

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kori jami’anta uku daga makarantar horar da ’yan sanda ta Ogida da ke Jihar Edo, saboda rashin da’a.

Kwamandan makarantar, ACP Bamidele Awoniyi ne ya bayyana hakan ranar Laraba, a bikin yaye kuratan ’yan sanda da aka dauka aiki a shekarar 2021.

Ya ce mata 149 ne da maza 290 suka samu horon daga jihohin Edo da Delta, sai dai an kori uku daga cikinsu saboda aikata laifin, wanda ya kama jimillar jami’ai 436 ke nan, maimakon 439.

Duk da kwamandan bai bayyana laifukan da jami’an suka aikata ba, ya ce biyu mata ne daya kuma namiji.

Shi ma Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce za a tura jami‘an kananan hukumomi daban-daban don ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Haka kuma a cewarsa dibar kuratan ’yan sanda 10,000 da ake yi duk shekara tsawon shekaru uku a Najeriya, na nuna kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na samar da rundunar tsaro mai karfi da za ta iya kai kasar ga ci.

Ya kuma shawarci jami‘an da su yi aiki da kwarewa a duk inda suka samu kansu, domin rundunar ba za ta lamunci karya dokokin aikin ba ko kadan.