✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kori kuratan sojoji 1,000 kan amfani da takardun bogi a Kamaru

An kori kuratan sojoji 1,000 a Kamaru saboda amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Akalla kuratan sojoji 1,000 ne aka kora a yayin da suke tsaka da karbar horon shiga aikin soji saboda amfani da takardun bogi a kasar Kamaru.

Ministan Tsaron kasar, Joseph Beti Assomo, ya sanar cewa an kori kuratan sojojin ne a wata makarantar bayar da horo.

Ya sanar a ranar Juma’a cewa kuratan da aka dauka a bana suna cikin samun horon shiga aikin soja ne aka gano sun yi amfani da takardun bogi.

Kakakin Rundunar Sojin Kasar Kamaru, Cyrille Guemo ya bayyana matakin da rundunar ta dauka a matsayin “bin diddigi’’ a cikin aikin soji.

Karo na farko ke nan da kasar Kamaru da ke yankin Tsaiyar Afirka ta kori kuratan sojoji masu wannan yawa saboda amfani da takardun bogi.