Hukumar kwastam ta kori jami’inta da ya yi fice a yaki da cin hanci da rashawa, ACG Bashir Abubakar, wanda shugaba Buhari ya karamma a shekarar 2019.
Hukumar ta kori mataimakin shugaban hukumar kwatsam Aminu Dahiru, ta kuma tilasta wa Bashir Abubakar ajiye aiki, wanda shi ma mataimaki ne ga shugaban rundunar ta kwatsam.
A sanarwar da kakakin hukumar DCP Joseph Attah ya fitar ta ce an dauki matakin a kan manyan hafsoshin ne bayan samun su da laifin sakaci da aiki a watan da ya gabata.
An tuhumi ACG Aminu Dahiru da hannu a badakalar fasakwaurin manyan motoci guda 295 makare da man fetur a watan Disamban 2019 a lokacin da yake aiki da Rundunar Kare kan Iyakokin kan Tudu na Kasa.
A shi kuma ACG Bashir Abubakar ana zarginsa da ba da umarnin yin samame a rumbun ajiyar shinkafa ‘yar gida a kokarinsa na gano shinkafar waje a rumbunan ajiyar wani fitaccen mutum a garin Daura, Jihar Katsina.
A watan Nuwamban shekarar 2019, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Hamid Ali suka karama Bashir Abubakar da lambar girmamawa bisa gaskiyarsa da kwazon aiki.
Bashir Abubakar ya kuma samu yabo daga hukumar a shekarar 2018 bayan da yaki karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka dubu 412 da wasu da suka shigo da miyagun kwayar Tramadol a lokacin da yake kula da rundunar a shiyar Apapa a Legas, lamarin da ya sa ya yi fice.
Kakakin hukumar ya kuma sanar tabbatar da nadin masu taimakawa shugaban rundunar guda biyar ta kuma yi wa manyan jami’anta 2,634 karin girma.