✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori hafsohin ’yan sanda 19 daga aiki

An kori hafsoshin ’yan sandan Nijeriya 19 daga aiki, an rage wa wani mataimakin Kwamishina da wasu 18 matsayi, bayan kama su da aikata laifi…

Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta kori mayan hafsoshin ’yan sanda 19 tare da rage wa wasu 19 mukami a ranar Juma’a.

Shugaban hukumar, AIG Haruna (murabu), ya ce, An yanke wa ’yan sandan hukuncin ne bayan samun da laifuka daban-daban da aka bincinke su a kai bayan an zarge su a aikatawa.

Wadanda aka kora sun hada da masu mukamin ASP guda 10 da DSP guda shid sai CSP guda biyu dakuma SP daya.

Ya bayyana cewa hukumar ta ba da takardar gargadi mai tsauri ga wani Mataimakin Babban Hafsan Dan Sanda kan rashin bin umarnin gudanar da aiki.

Sanarwar da kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce sauran hafsoshin ’yan sandan da aka rage wa matsayi sun kunshi Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda daya da CSP daya da SP biyu da DSP biyu da ASP 13.