An kori hadimin wani dan Majalisar Tarayya daga Borno daga aki saboda ya jinjina wa Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shakau.
An kori Bukar Tanda, hadimi ga Dan Majalisa mai wakiltar Birnin Maiduguri, Hon. Abdulkadiri Rahis, ne bayan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Shekau gwarzo ne wanda ya yi mutuwar jarumai, inda ya zabi ya kashe kansa da ya mika wuya ga abokan gaba.
“Ina yabo da jinjina ga Shekau bisa yadda ya kashe kansa; ya yi rayuwa irin ta jarumai, ya mutu a matsayin jan gwarzo yadda babu mai iya gano gawarsa,’’ a cewarsa.
Kalaman na Tanda sun bai wa jama’a mamaki ganin yadda ya yi su a daidai lokacin da sojoji ke zargin a cikin al’umma akwai masu nuna tausayi ga ’yan Boko Haram.
Sai dai maigidansa, Hon. Abdulkadir Rahis, ya fitar da sanarwa mai dauke da sanya hannunsa cewa ya sallami hadimin nan take.
Ya nesanta kansa daga kalaman hadimin wadanda ya ce sun sha bamban da matsayin al’ummar mazabarsa da ma jam’iyyarsa ta APC.
A makon jiya ne rahotanni suka ce Shugaban na Boko Haram, Abubakar Shekau ya kashe kansa bayan wani artabu da mayakan ISWAP, wanda reshen kungiyar IS ne a Yammacin Afirka.