✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kori dan sandan da ya shiga kungiyar asiri

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kori wani kurtun dan sanda mai suna  Mfon Esio wanda ta samu da laifin shiga kungiyar asiri. Mai…

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta kori wani kurtun dan sanda mai suna  Mfon Esio wanda ta samu da laifin shiga kungiyar asiri.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar CSP N-Nudam Frederick ya shaida cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edgal Imohimi ne ya ba da umarnin koran dan sandan bayan bincike ya tabbatar da cewa dan kungiyar asiri ne.

Ya ce korarren dan sandan na cikin wadanda suka tursasa wani mutum mai suna Ubong John William shiga kungiyar asiri ta Junior Vikings a ranar 20 ga watan Mayu, 2020.

“Korarren dan sandan na cikin wadanda suka tursasa mutumin shiga kungiyar asirin a wani daji da ke yankin Marina a karamar hukumar Eket da ke jihar Akwa Ibom.

“An dauki matakin korar dan sandan ne bayan bincike ya nuna cewa dan kungiyar asiri ne, kuma wannan mataki na zuwa ne domin kakkabe bata-gari a cikin rundunar ‘yan sanda”, inji shi.

Ya kara da cewa rundunar ta kame mutum 12 da ake zargi da shiga kungiyar asiri daga sassan jihar dauke da kananan bindigogin fistol kirar gida guda 10 da sauran makamai da suka hadar da adduna da kayayyakin tsubbace-tsubbace na kungiyoyin asiri.

Kwamishinan ‘yan sandan na Akwa Ibom ya jadadda aniyar rundunar na kakkabe duk wani bata-gari ba tare da la’akari da matsayinsa ko mukaminsa ba.