Hukumar gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Auchi (Auchi Poly) ta kori dalibai 40, bisa samun su da laifin gurbata sakamakon jarabawa.
Kakakin Kwalejin da ke Jihar Edo, Adebola Ogunbowa, ta sanar cewa an kori daliban ne bayan an bankado asirinsu yayin tatance daliban shekarar 2020/2021 da makarantar ta yi, kamar yadda ta saba yi duk shekara.
- Ortom ya gayyaci Buhari kaddamar da aiki a Benuwai
- ’Yan bindiga sun harbi fasto, sun sace tsohuwar Akanta-Janar
Ta ce yayin binciken an gano yadda daliban suka samu guraben karatun Karamar Difloma (ND) da Babbar Difloma (HND) a makarantar da sakamakon jabu.
Baya ga haka, daliban ba su cika wasu ka’idoji da Kwalejin ta shimfida ga masu neman gurbin karatu a cikinta ba.
Ta kara da cewa Shugaban Makarantar, Dokta Salisu Umar ya gabatar da sabbin kwasa-kwasai 12 da za a fara koyarwa a kwalejin a shekarar 2023.