Wasu fusatattun matasa sun banka wa wani mutum da ake zargi da satar babura tare da kone shi kurmus a garin Ile-Ife na jihar Osun.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ’yan acaba ne suka kama wanda ake zargin da ba a kai ga tantance wane ne ba a unguwar Ilode dake yankin Ile-Ife jim kadan da kwace wani babur.
- Fusatattun matasa sun kone mutum 3 kurmus bisa zargin garkuwa
- Boko Haram ce ta yi garkuwa da daliban Kankara —Shekau
Wannan dai shine karo na uku da mutane ke daukar doka a hannunsu cikin kwanaki tara a jihar, inda ko a ranar Juma’a, hudu ga watan Disamban 2020 sai da wasu ’yan acaba suka kone wasu mutum biyu da ake zargi da irin wannan laifin a unguwar Lager eta Ile-Ifen.
Bugu da kari, ko a aranar Alhamis, 10 ga watan Disamba sai da aka kone karin wasu mutum biyu da ake zargi da kasancewa masu garkuwa da mutane a yankin Iwo.
A ranar Lahadin da ta gabata ma a yankin Ilode, ’yan acaban sun lakada wa wani wanda ake zargi dukan kawo wuka daga bisani kuma suka cinna masa wuta.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, Yemisi Opalola ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin inda ta ce lamarin ya faru ne gabanin zuwan jami’ansu.
Ta ce, “Daga bayanan da muka tattara, an kama wani wanda ake zargi da kasancewa dan fashi a Oko-Igbo dake unguwar Ilode a garin Ile-Ife bayan ya kwace wa wani babur.
“Daga bisani wasu ’yan acaba suka bi shi tare da banka masa wuta kafin zuwan ’yan sanda,” inji ta.