A safiyar Litinin wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun cinna wuta a Ofishin Yakin Neman Zaben dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Mohammed Jibrin Barde.
A yayin da wutar ke ci, kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da harin da aka kai a ofishin da ke kusa da Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.
- Ku yi hattara da romon bakan Atiku —Tinubu ga ’yan Najeriya
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi
Sai dai PDP ta zargi Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da hannu, tana mai cewa “’Yan daba sun kai hari Oifhin Yakin Neman Zaben Barde da sanyin safiyar yau Litinin, kuma muna zargin APC na da hannu a ciki.
“Wannna harin daya ne bayan wasu da dama da aka kai mana a ’yan watatnnin nan, wanda ke nuna gwamnatin nan ta dauki salon tashin hankali, kuma dole ne a yi tir da shi,” in ji Mataimakin Kakakin Yakin Neman Zaben Atiku/Barde a Jihar, Junaidu Usman Abubakar.
Sanarwar da ya fitar a safiyar Litinin ta bayyana cewa an yi asara mai yawa a ofishin da aka cinna wa wuta.
Wakilinmu ya tuntubi Ismaila Uba Misilli, Darakta-Janar na Yada Labaran Gwamna Inuwa Yahaya, kan lamarin, amma ya ce zai waiwaye shi daga baya.
Amma Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatar da harin, tare da cewa sun fara bincike da nufin cafko maharan.
Aminiya ta gano duk da yarjeneniyar zaman lafiya da ’yan siyasar jihar suka sanya hannu a kai gabanin zaben 2023, an samu karuwar rikicin siyasa a jihar.
Shi kansa ofishin na PDP da aka kona, a watan Agusta an kai masa hari tare da farfasa shi.