Rahotanni sun bayyana cewa mutane biyar sun rasu, sannan yara uku sun bata, biyo bayan rikicin da ya barke inda wasu bata gari suka shiga satar kayan mutane a garin Kalaba.
Mutane uku sun rasu ne a sakamakon tashin wuta da ya ritsa dasu a ofishin Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta jihar Kuros Riba, biyu kuma sun rasu ne a sanadiyar cinkoso yayin da ake tsaka da sata da wawason kayan abinci.
- Buhari ya fadi adadin mutanen da aka kashe a zanga-zangar EndSARS
- EndSARS: Dalilin da ya hana Buhari magana a kan harbin Lekki
- #EndSARS: An shawarci ‘yan kasuwa su kauracewa zuwa Legas
- A kiyayi kai wa Musulmi hari da sunan #EndSARS —NSCIA
Bankin First Bank da kuma Ofishin saida wayoyi na kamfanin Tecno duk an cinna musu wuta bayan da aka yashe su.
Rikicin ya janyo saka dokar hana fita na sa’o’i 24, tare da hana jami’an tsaro harbin wanda suke satar kayan abincin domin kaucewa tashin hankalin da ba a shirya masa ba.
Har wa yau, bata garin sun kona motoci biyu na Editan jaridar Nigerian Chronicles Mista Sam Egbala, tare da awon gaba da kayayyakin wasu daga cikin ma’aikatan gidan jaridar.