An killace Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai da wasu manyan hafsoshin rundunar bayan cutar COVID-19 ta kashe Babban Kwamandan Runduna ta 6 Johnson Olu Irefin a lokacin taron da suke halarta.
Buratai ba zai samu halartar daurin auren dansa Hamisu, da za a yi ranar Juma’a ba sakamakon killacewarsa da manyan hafsoshin rundunar da suka halarci taron, bayan rasuwar Manjo Janar Irefin.
- Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari
- COVID-19 ta kashe Janar din Sojin Najeriya
- El-Rufai zai dawo da dokar kulle a Kaduna idan…
“Shugaban Rundunar Sojin Kasa da iyalansa na matukar godiya da kuma maraha da daukacin mahalarci daurin auren dansa,” inji kakakin rundunar, Birgediya Sagir Musa, tare cewa za a ci gaba da sha’anin daurin auren ba tare da shagulgula ba, yayin da uban ango ke a killace.
Manyan hafsoshin sojin na halartar taron ne sa’ilin da daya daga cikinsu, Manjo Janar Irefin ya nuna alamar COVID-19 wadda ta kai ga an kai shi asibiti a Abuja, inda a nan rai ya yi halinsa.
A safiyar Alhamis Rundunar ta soke ci gaba da taron na shekara-shekara wanda Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya halarci zauren, Shugaba Buhari kuma ya bude taron daga ofishinsa ta bidiyo.
Kawo yanzu dai babu bayanin ko Ministan Tsaron ya killlace kansa, yayin da rundunar sojin ta umarci maharta taron da su killace kansu na kwana 14.
Mutuwar Manjo Janar Irefin ta jawo fargabar harbuwar wasu mahalarta taron da kwayoyin cutar ta coronavirus wadda Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya ce guguwar annobarta ta sake tasowa a karo na biyu a Najeriya sabod rashin bin matakan kariya.
Shugabannin addini na da hannu a karuwar cutar
Gwamnatin Tarayya na zargin wasu kungiyoyin addinai da ke shirya taruka da yin kafar ungulu ga shirin na dakile yaduwar cutar a Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa (PTF) kan Yaki da COVID-19, Boss Musatapha ya bayyana haka yayin jawabin hadin gwiwar da kwamitin ya saba gudanarwa.
“Abin taikaici shi ne yadda wasu kungiyoyin addinai ke ci gaba da gudanar da manyan tarukan da gangami da ke iya yada cutar.
“PTF na rokon dukkan matakannin gwamnati da kungiyoyin suka sanya hannu a wurinsu kan kiyaye matakan kariyar cutar da su zage damtse wurin aiwatar da dokokin kariyar”, inji Boss Mustapha.
Ya ce PTF za ta yi ta tuntubar masu ruwa da tsaki kan tasirin COVID-19 da suka shafi lafiyar kwakwalwa, cin zarafin jinsi da kuma shan miyagun kwayoyi.
“Annobar na kara ruguza harkokin jama’a. Dazu muka samu rahoton rufe taron wata rundunar tsaro ba shiri bayan an gano daya daga cikin mahalarta ya kamu da COVID-19.
“Wannan ya nuna muhimmancin matakan yaki da cutar da ake bi a kasa, don haka, muna rokon ’yan Najeriya da masu shirya taruka da su rika yin gwaji da tantance mahalarta”, a cewarsa.
Shirin samar da rigakafin COVID-19 a Najeriya
Ya ce yayin da gwamnati ke kokarin samarwa da kuma amfani da rigakafin cutar, wajibi ne ’yan kasa su rika kiyayewa domin takaita yaduwar cututtuka da mace-mace
Mustapha ya ce nan da mako biyu masu zuwa PTF za ta gabatar wa Shugaban Kasa rahotonta na karshe.
Sai dai ya ce hakan ba ya nufin aikin ya kare, saboda har yanzu da sauran rina a kaba wurin ganin bayan cutar a Najeriya.
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, a nasa bangaren, ya ce bayan sake bazuwar cutar ta coronavirus a Najeriya, gwamnati na shirin sayen rigakafi domin yi wa mutum miliyan 20 a kasar.
Ministan ya ce za a yi rigakafin ne ga jami’an lafiya da mutane masu rauni da suka fi hadarin kamuwa da cutar.
El-Rufai ya yi barazanar dawo da dokar kulle
Tuni dai Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi barazanar sanya dokar kulle bayan karuwar masu kamuwa da cutar a Jihar.
El-Rufai ya ce muddin jama’a suka ba sa sanya takunkumi, bayar da tazara da kiyaye matakan kariyar cutar, to ba shi da zabi face ya dauki matakai, ciki har da sanya dokar kulle.
Kakakin El-Rufai, Muyiwa Adeleke, a cikin wata sanarwa ya ce , “Daga watan Agusta zuwa Satumba alkaluman kamuwa da cutar na raguwa da kashi ,1%, 2%, 3% amma yanzu ya yi tashin gwauron zabo zuwa kashi 20% da 35%”.
Mai taimaka wa Gwamnan a kafofin watsa labarai, Abdallah Yunus Abdallah, ya ce kare dukiyoyi da rayukan al’umar jihar wajibi a kan gwamnan, shi ya sa ya yi wannan jan kunnen.
Abdallah, ya ce tabbas gwamnan zai sake sanya dokar zaman gida muddin jama’a suka ki kiyaye hanyoyin hana yaduwar cutar aka kuma ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da ita.
’Yan Najeriya na karya matakan kariya
Baya ga Kaduna an samu wasu jihohi da yanayin kamuwar mutane da cutar ke ta hauhawa.
Masana kiwon lafiya sun dora laifin hakan a kan watsi da matakan kariya da jama’a ke yi.
Aminiya ta gano cewa ’yan Najeriya da dama sun daina bin matakan kariyar coronavirus da gwamnati ta sanya a farkon bullar cutar.
Yanzu yawancin mutane sun daina sanya takunkumi, bayar da tazara, tsaftace hannu da sauran matakan kariyar cutar.
A wata 10 na farko da cutar ta bulla a Najeriya, wasu sun yi ta musanta samuwarta baya ga bayanan karya da aka yi ta yadawa a kanta.
A watanni biyu da suka gabata, masana kiwon lafiya da hukumomin da ke da alhaki a kasar sun yi ta gargadin yiwuwar sake bazuwar cutar coronavirus daga baya saboda mutane sun yi watsi da matakan kariya.
A ranar Talata kadai mutum 550 ne suka kara kamuwa da COVID-19 a Najeriya; 219 daga cikin adadin Legas kadai, sai Abuja da mutum 168.
A cikin makon farko na watan Disamba kadai mutum 694 ne suka kamu cutar a Jihar Legas.
Kawo yanzu mutum 70,669 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya; 65,242 daga cikinsu sun warke, 1,184 kuma sun mutu.