Mahukunta a Saudiyya sun kawo karshen dokar bayar da tazara da aka kakaba sakamakon annobar Coronavirus a Masallatai biyu mafi daraja a ban kasa da ke Makkah da Madina.
Shugaban Majalisar Masu Kula da Masallatan Biyu kuma Babban Limamin Masallacin Ka’abah, Sheikh Abdurrahman Al-Sudais ne ya sanar da daukar wannan mataki a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce daga gobe Lahadi, 11 ga watan Rabi’ul Awwal, za a fara bai wa masu ibada damar shiga masallatan biyu ba tare da takaitawa ba.
Wannan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida ta bayar da umarnin bude masallatan biyu gaba daya da kuma sassauta matakan kariya da aka dauka.
Bayanai sun tabbatar da cewa, da wannan sabon mataki, za a bari mutane su gudanar da ibada ba tare da wani shamaki ba wurin Dawafi da Safa da Marwa.
Sai dai har yanzu Saudiyya ta ce dole ne sai wanda ya kammala karbar allurar rigakafin Coronavirus guda biyu kafin shiga masallatan.
Kazalika, hukumomin sun ce har yanzu dokar sanya takunkumin rufe hanci da baki na nan ga baki masu ibada da kuma maaikatarn da ke kula da masallatan.
Alkaluman sun ce cutar Coronavirus ta harbi mutm 547,845 da kuma hukumomi suka tantance a Saudiyya tun bayan barkewarta.
Haka kuma alkaluman sun nuna cewa cutar ta yi ajalin mutum 8,758 daga cikin wadanda ta harba sannan fiye da dubu 500 sun warke.
Annobar da ta mamaye duniya ta yi sanadiyar takaita aikin Hajji bara da bana, abinda ya hana maniyata daga kasashen duniya zuwa aikin ibadar.