Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya sanar da cewa an kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, tare da kama wasu mutum biyu da ke da hannu a sace ɗaliban likitanci 20.
Ya miƙa ɗaliban ga shugabannin Jami’arsu a Abuja ranar Lahadi, inda ya tabbatar da cewa waɗanda aka kama suna hannun ’yan sanda.
- Amnesty ta soki Gwamnatin Sokwato saboda kama wani dan soshiyal midiya
- ’Yan sanda na farautar ’yan Shi’a kan Kisan ’yan sanda a Abuja
An sace ɗaliban ne ranar 15 ga watan Agusta a Jihar Benuwe, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Enugu.
A ranar 22 ga watan Agusta, ’yan sanda suka ceto ɗaliban tare da wasu fasinjoji biyar da kuma wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu a sace ɗaliban.
An ceto ɗaliban ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Egbetokun, ya bayyana cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar yayin wata musayar wuta da ’yan sanda, kuma an kama wasu ’yan ƙungiyarsa biyu, tare da ƙwace makamansu.
Waɗanda aka kama suna hannun ‘yan sanda a yanzu haka, inda ya ce suna bayar da bayanan da za su taimaka wajen sake kama wasu.
Sufeton ya ce ceto ɗaliban ya ba su wahala, domin jami’ansa na buƙatar manyan kayan aiki.
Egbetokun, ya nuna godiyarsa ga Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da sauran hukumomin tsaro da suka taimaka wajen nasarar ceto ɗaliban.
Ya jaddada cewa nasarar ceton ɗaliban na nuna abin da za a iya cimma ta hanyar aikin haɗin gwiwa domin cimma burin da aka sa gaba.