Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda uku na kungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi a Jihar Borno.
An kashe ’yan ta’addar ne a yayin da sojoji ke gudanar da hare-hare a gabar tafkin.
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur?
- Umarni 14 da sabon Gwamnan Kano ya bayar bayan rantsar da shi
Wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a yankin, Zagazola Makama, ya bayyana a Maiduguri cewa “Sojojin bataliya ta 86 a gefen Malam Fatori da ke a Karamar Hukumar Abadam, sun yi nasarar kashe ’yan ta’addan a ranar Lahadi, 28 ga Mayu, 2023.”
A cewarsa, sojojin sun kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu daga hannun ’yan ta’addan da suka tsere.
Wata majiyar soji a Maiduguri ta ce wani soja ya samu rauni a lokacin arangamar, inda ta ce: “An kwashe ma’aikatanmu da suka ji raunuka, an garzaya da su asibitin sojoji da ke Maiduguri domin kula da lafiyarsu.