Wasu masu tayar da zaune tsaye da ake zargi ’yan Boko Haram ne sun kai hari tare da kashe wasu mutum uku a wani shingen bincike ababen hawa da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Gubio da tsakar ranar Lahadi.
Wani babban jami’in kungiyar sa-kai, Bakura Aliyu ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantarwasa da wakilanmu.
- Sabbin Manyan Hafsoshin Soji sun kai ziyara Maiduguri
- NDLEA ta kama mace da hodar Iblis ta N30bn
- COVID-19: An sanar da ranar sake bude makarantu a jihar Filato
Mun rasa mutum uku ciki har da dan kungiyarmu guda daya da jami’an ’yan sanda biyu yayin da maharan suka kawo farmaki sansanin binciken wanda suka kona wata mota kirar Hilux guda daya sannan suka arce da wata,” inji Bakura.
Rahoton da Aminiya ta samu ya bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun kai farmaki sansanin binciken da ke tsakanin yankin Chabol da Magumeri da misalin karfe 12.30 na rana, inda suka kashe wasu jami’an ’yan sanda biyu da wani dan kungiyar sa-kai yayin da suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Wata majiyar ta shaida wa wakilanmu cewa maharan sun kuma kone wata motar sintiri yayin da suka arce da guda daya bayan sun tarwatsa jami’an tsaron da ke sansanin binciken.
Majiyar ta ce, “wannan lamari ya faru a tsakanin da Magumeri da Chabol, kuma mun samu rahoton cewa jami’an ’yan sanda biyu da wani dan kungiyar sa-kai guda daya sun rasa rayukansu a harin na kwanton bauna.”