✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ‘yan Boko Haram 411 a Borno

A kalla ‘yan Boko Haram 411 ne aka kashe bayan wani hari da aka kai musu da jiragen sama a wasu kauyuka a Arewacin Borno.…

A kalla ‘yan Boko Haram 411 ne aka kashe bayan wani hari da aka kai musu da jiragen sama a wasu kauyuka a Arewacin Borno.

Wasu ‘yan banga da aka fi sani da JTF suka shaida wa wakilinmu a Maiduguri cewa an yi wa ‘yan Boko Haram din diran mikiya ne a kauyen Gudumbali.

An samu labarin cewa ‘yan Boko Haram sun kwashe kusan mako biyu suna taruwa a kauyen da nufin kai wasu hare-hare da suke shiryawa.

“A ranar Asabar da ta gabata, an kai wa Boko Haram hari ta sama a sansanoninsu guda 9, inda aka kashe kusan 350 daga cikinsu,” inji jami’in JTF din.

Hakanan kuma a kauyen Musune da ke Karamar Hukumar Dikwa, an kashe wasu ‘yan Boko Haram din guda 61.

Wani mai gadi a Dikwa, Malam Haruna Ahmed ya ce “A ranar Juma’a, sojojin sun ma ‘yan Boko Haram kwantar bauna, inda suka kashe guda 61, kuma suka kwace wasu makamai,” inji shi.

A sansanin sojoji kuma da ke Karamar Hukumar Marte, an ce an kashe sojoji guda 9 “A ranar Alhamis da misalin karfe 5 na yamma, wasu ‘yan Bindiga sun far wa sojoji, inda suka bude musu wuta har suka kashe sojoji 9, sannan kuma suka jikkita wasu da dama,” inji wani dan banga.

Har yanzu dai ba a samu wani sanarwa ba daga rundunar sojoji a kan harin.