✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan bindigar da suka sace matar Kwamishina a Binuwe

Duk da nasarar da aka samu ta ceto su, matar kwamishinan ta jikkata.

Jami’an ’yan sanda a Jihar Binuwe sun harbe wasu masu garkuwa da mutane uku a kokarin ceto wata mai dakin Kwamishina da aka sace kwanaki hudu da suka gabata.

A ranar Alhamis da ta gabata ce ’yan bindiga suka yi awon gaba da Ann Unenge, Matar Kwamishinan Kasa da Safiyo na Jihar tare da direbanta a Makurdi, babban birnin Jihar.

An sace matar ce bayan kasa da mako daya da aka yi awon gaba da wasu matan aure biyu ciki har da matar wani likita a Unguwar Sabuwar GRA da ke babban birnin jihar.

Bayanai sun ce an sako matan auren biyu bayan ’yan uwansu sun biya kudin fansa na Naira miliyan shida.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce ’yan bindigar suka nemi kudin fansa na naira miliyan 51 domin sako matar kwamishinan da suka sace, inda yayin wata musayar wuta da ’yan sanda a yammacin Litinin mutum ukun da suka yi garkuwa da ita suka ce ga garinku nan.

Sai dai duk da nasarar da aka samu ta ceto su, Ann da direbanta sun jikkata inda a halin yanzu suke karbar magani a Asibiti.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene da ta tabbatar da faruwar hakan, ta ce zuwa gaba za ta fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya kasance.

Gwamna Samuel Ortom wanda ya jagoranci wata tawaga ta ’yan Majalisar Zartarwa zuwa Hedikwatar ’yan sandan Jihar inda aka jibge gawawwakin ’yan bindigar da aka kashe, ya yaba wa kwazon Babban Sufeton ’Yan sanda da sauran jami’ai dangane da wannan nasara da aka samu a Binuwe.