’Yan bindiga akalla 200 sun sheka lahira a wata ragargaza da jami’an tsaro suka yi wa gungun ’yan bindiga da Bello Turji da takwarorinsa suke jagoranta a Jihar Neja.
Jami’an tsaron sun aika ’yan bindigar sama da 200 ne a cikin kwana hudu da suka shude, inda suka yi da yi wa bata-garin luguden wuta babu kakkautawa a jihar.
- Medinat Abdulazeez Malefakis: Gwanar yaki da ta’addanci
- Za a kashe N3bn wajen kwaso ’yan Najeriya da suka mukale a Ukraine
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Emmanuel Umar, ya bayyana cewa daga cikin gungu-gungun ’yan bindiga da jami’an tsaro suka tarwatsa a jihar har da wadanda kasurguman ’yan bindigar nan Bello Turji, Yellow Janbros, Kachalla Halilu da Ali Kawaje suke jagoranta.
A baya-bayan nan dai, ’yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a sassan Jihar Neja suna aikata kisan gilla gami da garkuwa da mutane da kuma kone-kone.
Kwamishinan ya sanar a wani taron karawa juna sani kan harkar tsaro a jihar cewa duk da haka wasu daga cikin bata-garin sun tsere da raunukan harbi a jikinsu.
Ya ce kayan da aka kwato a hannun ’yan bindiar da aka ragargaza sun hada makamai da babura da shanu da sauran abubuwa.
Sai dai Umar ya ce amma an yi rashin sa’a, jami’an tsaro biyu sun kwanta dama a lokacin gumurzun da aka tafka da ’yan bindigar.
Ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Neja a shirye take ta shiga yaki tsakaninta da ’yan ta’adda masu addabar jihar.
Sannan ya jinjina wa daukacin jami’an tsaro, al’ummar jihar da kafafen watsa labarai game da yadda suke taimakon gwamnatin jihar wajen yaki da ta’addanci.