✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan bindiga a wurin karbar kudin fansa

Mafarauta sun ceto mutumin da aka sace bayan kashe ’yan bindigar.

Mafarauta sun aika wasu ’yan bindiga lahira a yayin da suka je karbar kudin fansar wani mutum da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kogi.

Mafarautan sun bindige ’yan bindgiar ne a yankin Abobo na jihar, inda bata-garin suka je karbar kudin fansa a ranar Talata.

Ba su yi wata-wata ba, suka aika biyu daga cikin ’yan bindigar lahira, ragowar dayan kuma ya tsere zuwa cikin daji dauke da raunin harbi, suka kuma kubutar da mutumin da aka yi garkuwa da shi.

Da yake magana da manema labarai, jami’in dan sanda mai kula da yankin Okehi, ya ce an tura karin ’yan sanda su mara wa mafarautan baya wurin cafko daya dan bindigar da ya tsere.

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ta hannun Sakataren Yada Labaransa, ya ce gwamnatinsa ba za ta raga wa ’yan ta’adda ba.

Ya ce an zabe shi ne domin ya kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kogi, don haka zai cika alkawuran da ya dauka.

Gwamnan ya kuma jinjina wa mafarauta kan namijin kokari da suka yi na ceto mutumin da aka sace tare da inganta yanayin tsaro a jihar.