✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ‘yan bindiga 9 tare da kame wasu a Jihar Neja

Akalla 'yan bindiga tara ne suka sheka lahira a gumurzun da suka da yi da 'yan banga a jihar Neja.

Akalla ’yan bindiga tara ne suka sheka lahira a wani gumurzu da suka da ’yan banga a yankin Azza dake karamar hukumar Lapai, a jihar Neja.

Aminiya ta gano an yi dauki ba dadin ne a ranar Lahadi, yayin da wasu mutum biyu suka hadu a daji domin kai kudin fansar ’yan uwansu.

Bayan kai kudin fansar ne, ’yan bindigar suka umarce su da su sayo musu kayan abinci da suka hada da shinkafa, burodi, garin tuwo, da katin waya, bayan fitar mutanen sai suka shaida wa ’yan banga abin da ke faruwa.

Wata majiya da ta shaida mana yadda abun ya faru, ta ce ’yan bangar sun yi shiri na musamman ne inda suka farmaki ’yan bindigar.

An dauki tsawon awanni ana dauki-ba-dadi, wanda ya yi sanadin rasa hallaka ’yan bindiga tara.

Wani mazaunin yankin Gulu, yayin tattaunawa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Abasar, ya bayyana, yadda wata mata ta kubuta tsirara daga hannun ’yan bindigar, sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi.

Matar, ta bayyana yadda ’yan bindigar suka daure su maza hudu mata uku a jikin bishiyoyi.

Wata majiyar ta bayyana cewa rahoton da matar ta bayar a gidan mai garin Gulu ne ya taimaka wa ’yan banga samun nasara a kan ’yan bindigar.

Sai dai an yi rashin sa’a ’yan bindigar sun kashe mutane hudu a yayin artabun.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun, bai dauki wayar wakilinmu ba, bare mu ji ta bakinsa kan lamarin.