Mahukunta sun tabbatar da cewa wani hari ta’addanci ya hallaka sojoji 15 a ƙasar Mali da ke Yammacin Afirka.
Kamar yadda hukumomin sun suka tabbatar, an ɗora alhakin harin a kan ƙungiyar da ke da alaƙa da Al-Qaeda.
“Aƙalla sojojin Mali 15 aka kashe a ranar Alhamis a yayin wani harin kwanton-ɓauna da masu iƙirarin jihadi daga ƙungiyar Support of Islam and Muslims suka kai,”.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da wani zaɓaɓɓen jami’in gwamnati daga yankin Mopti ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP inda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda yanayi na tsaro.
Majiyar ta ƙara da cewa akwai wasu “sojoji da suka ɓace da kuma jikkata.”
Haka kuma akwai wani zaɓaɓɓen shugaba da ya tabbatar da wannan labarin, inda ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai “sojoji 14 da jandarma ɗaya.”
“Akwai sojojin da suka ɓace, maharan sun kuma ƙwace kayayyakin yaƙi,” kamar yadda majiyar ta ƙara da cewa.
Haka kuma wani jami’i na daban ya shaida cewa an kai harin ne kilomita biyar daga ƙauyen Diallassagou.
Ya ƙara da cewa “akwai sama da mutum 10 waɗanda suka ji rauni sannan sama da 15 suka rasu a sojojin Mali”.
Mali ta shafe sama da shekara 10 tana fama da rikicin masu iƙirarin jihadi da na wasu ƙungiyoyin.