✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe sojoji 10 a Arewacin Siriya

Ana fargabar adadin zai iya karuwa saboda yawan wadanda suka jikkata

Sojoji 10 ne suka hallaka a Arewacin Siriya, tara kuma suka jikkata, bayan an harba wa motarsu makami mai linzami a ranar Juma’a.

Kamfanin dillancin labarai na kasar, SANA, ne ya rawaito cewa Rundunar Sojin Kasar ta fitar da wata sanarwa da ke bayyana cewa yan ta’adda sun harba makamin kan motar da ke yankin Anjara na Arewacin kasar  wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin 10.

A hannu guda kuma hukumar  da ke sanya ido kan kare ’yancin dan Adam ta Birtaniya reshen kasar ta  Siriya,  ta ce wadanda aka kashe din na daga cikin ’yan gaba-gaban mayakan da ke goyon bayan gwamnati.

Kazalika hukumar ta ce akwai yiwuwar samun karin mamatan, la’akari da yawan wadanda suka samu munanan raunuka sanadiyyar harin.

Harin dai shi ne na baya-bayan nan da aka kai daga jerin hare-haren da ake kai wa kan sojojin kasar .

Ko a ranar 13 ga watan Maris ma dai, sai da aka kashe sojoji 13 a wani wani harin kwanton bauna da aka kai wani kauye da ke tsakiyar lardin Homs.