✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe sabon shugaban ISWAP, Malam Bako

Monguno ya ce sojoji sun hallaka Malam Bako kwana biyu da suka gabata.

Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da mutuwar sabon shugaban kungiyar ISWAP, Malam Bako, wanda ya gaji Abu Mus’ab Al-Barnawi da aka kashe.

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Mongonu, shi ne ya sanar da kashe Malam Bako bayan zaman da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi da shugabannin tsaro a ranar Laraba.

Monguno ya ce, “Sojojin kasa sun yi abin a yaba musu domin a cikin wata dayan da ya wuce sun kashe Shugaban ISWAP – wato Abu Mus’ab Al-barnawi.

“Kwana biyu da suka wuce kuma sojoji suka kashe magajinsa, Malam Bako, wanda shi ma babban mamba ne a majalisar shura a kungiyar.

Monguno ya kara da cewa, “A halin yanzu rikicin shugabanci ya dabaibaye kungiyar ISWAP. Kamar yadda kuka sani ne, irin wannan abu na tattare da matsalar yarda, rikici da kuma rashin yarda da juna da sauransu.

“Saboda haka ayyukan da sojoji suke yi a yankin Arewa ya matsa lamba ga ISWAP da Boko Haram da wata kungiya mai suna Islamic State in the Greatest Sahara.’’

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga watan Oktoban da muke ciki ne Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da mutuwar Abu Mus’ab Al-Barnawi.

A lokacin, Irabor ya ce: “Ina shaida muku da babbar murya cewa an kashe Abu Musab.’’