✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mutum shida ’yan gida daya a Filato

Cikin wadanda aka kashe har da mutum shida ’yan gida daya.

Mahara sun kashe mutum bakwai da tsakar dare a unguwar Dong da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

’Yan bindigar sun kai farmakin ne a ranar Lahadi, washegarin harin da aka kashe makiyaya biyu a unugwar Rantaya.

“Da misalin 11:30 na dare suka shigo, mutane na barci, suka fara harbi ta ko’ina. Da farko sun kashe mutum daya sannan suka shiga wani gida suka kashe mutum shida ciki har da matasa biyu,” inji wani dan unugwar Dong.

A ranar Lahadin da safe ma an kashe wasu mutum biyu a kauyen Kuru da ke Karamar Hukumar.

Kafin nan, ranar Alhamis an ba da rahoton bacewar mutum daya a kauyen Maiyanga da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar.

Akalla shanu 52 ne kuma aka harbe har lahira a hare-haren a Kananan Hukumomin biyu.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel, ya ce sun samu rahoto cewa, “’yan bindiga sun yi wa kauyen Dong dirar mikiya suka kashe mutum bakwai.

“An tura jami’an tsaron hadin gwiwar ’yan sanda da ’yan banga karkashin jagorancin wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, amma kafin su isa wurin bata-garin sun tsere.”

Ya ce ana ci gaba da kokarin damko maharan sannan an tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana barkewar rikici.