✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filato: An kashe mutum hudu a sabon hari

An kai harin kwana biyu bayan an bindige wani makiyayi.

Mutum hudu sun sheka lahira a wasu sabbin hare-hare da aka kai wa ’yan kabilar Irigwe a Jihar Filato.

Maharan sun kuma jikkata wasu mutane a hare-haren biyu da aka kai a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar a ranar Talata.

Mai magana da yawun ’yan kabilar Irigwe, Malison Davidson, ya ce mutum biyu na farkon an yi musu kwanton bauna an kashe su ne a hanyarsu ta zuwa gida, sauran kuma an kashe su ne a gona.

“An yi wa ’yan kabilar Irigwe uku kwanton bauna da misalin karfe 6:50 na yammacin Talata, 28 ga Satumba, 2021 a kan hanyar Twin Hill, da ke Jebbu Miango na Masarautar Miango a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.

“Nan take mutum biyu suka sheka lahira, na ukun kuma ya tsira da raunin harbin bindiga, an kuma garzaya da shi zuwa asibiti. Babur din kuma an kona shi.

“A yammacin ranar kuma an kashe wasu mutum biyu a gona aka kuma aka jikkata wasu”, inji shi.

Mun nemi samun karin bayani daga rundunar samar da taro ta Operation Safe Haven da ke Jihar Filato, amma har muka kammala hada wannan rahoto hakarmu ba ta cim ma ruwa ba.

Hare-haren na zuwa ne kwana biyu bayan an bindige wani matashi makiyayi a Kafigana da ke yankin nan Jebu.

Al’ummomin Fulani da Irigwe na yawan zargin junansu da kai wa juna hare-hare a kauyukan Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.