Kimanin mutum 80 ne suka mutu a hare-hare biyu na ’yan boko haram da kuma na kabilanci a jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin Najeriya.
Inda aka fi samun mace-macen shi ne a garin Mubi inda dan kunar-bakin-wake ya kashe mutum 50 a masallaci.
Mutum 30 sun mutu yawanci mata da yara a wani harin wanda kabilar Bachama da ke dauke da makamai suka kai wa Fulani a garin Numan.