An kashe mutum shida, an jikkata wasu da dama a kauyen Utai na Karamar Hukumar Wudil ta Jihar Kano, yayin karashen zaben ranar Asabar.
Lamarin ya faru ne lokacin da ake kokarin karasa zaben kujerar dan Majalisar Dokokin Jihar, wanda a baya Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana a matsayin wanda bai kammala ba.
A cewar wani ganau, rikicin ya fara ne a kauyen bayan an fara zabe a rumfar zabe daya kacal mai kasa da mutum 600, inda wasu ’yan daba da ake zargin an dauko hayarsu ne zuwa kauyen suka yi kokarin hargitsa zaben.
Ana dai karasa zaben ne tsakanin ’yan takara biyun da ke kan gaba a zaben, Nuhu Abdullahi na APC da kuma Ali Abdullahi Manager na NNPP, inda daga bisani aka ayyana dan takarar na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Da yake zantawa da Aminiya, wani mazaunin yankin, Dan-Asabe Sulaiman, ya ce galibin wadanda aka kashe ba ’yan kauyen nasu ba ne, hayarsu aka dauko daga wasu wuraren domin su hargitsa zaben.
Ya ce dama mazauna kauyen na sane da shirin da wasu ’yan siyasa suka yi na kawo ’yan daba, inda suka yi shirin ko-ta-kwana.
Ya kuma ce an kona motoci uku a yayin rikicin.
Shi ma wani ganau din a yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mutanen da aka kashe din sun kai tara.
Majiyar ta ce ragowar mutum uku da aka kai asibiti su ma daga bisani sun mutu, inda ya ce daya daga cikin mamatan ma yankan rago aka yi masa.
Bugu da kari, wata majiyar ma ta ce an sami makamancin wannan rikicin a Karamar Hukumar Garko wacce ke da makwabtaka da Wudil din, inda a can ma bata-gari suka kone motoci uku, kodayake ba a sami asarar rai ba.
Da aka tambayi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Abdulahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiran waya da rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike masa ba kan batun, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.