✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 5 a rikicin ’yan caca Akwa Ibom

An kusa sa'a hudu ana gumurzu a rikicin cacar tsakanin kungiyoyin asiri a ranar Talata, kafin ’yan sanda suka tarwatsa su

Rahotanni sun nuna akalla mutum biyar sun mutu, wasu da dama sun jikkata sakamakon rikicin da ya barke kan caca a garin Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Shaidu sun ce an shafe kusan sa’a hudu ana gumurzu a rikicin cacar da ya barke tsakanin ’yan kungiyoyin asiri Vikings da kuma Mafians yammacin ranar Talata, kafin daga bisani ’yan sanda suka tarwatsa bata-garin.

Wani ganau ya fada wa manema labarai cewa, rikicin ya samo tushe ne daga wani shagon caca a yankin Ikot Ekpene bayan jayayya ta shiga tsakaninsu.

Ya ce dan kungiyar Vikings ne ya buga cacar N5,000, amma ya kasa biyan kudin, aka bukaci ya mika wayarsa nan ma ya ki.

Ana tsaka da haka ne sai ya kira ’yan uwansa a waya, suka zo suka lakada wa mai tsaron shagon duka sannan suka lalata shagon.

Ya kara da cewa, daukar matakin ramuwa da ’yan kugiyar mai tsaron shagon ta Mafians suka yi ne ya haifar da barkewar rikici a tsakanin bangarorn biyu.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Odiko Macdon, ya tabbatar da faruwar hakan, sai dai bai bayyana adadin wadanda suka mutu a rikicin ba.