An kashe mutum hudu a wani rikici tsakanin mabiya akidar Shi’a da jami’an tsaron Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna.
An yi arangamar ne a lokacin da aka yi kicibus tsakanin ’yan Shi’a da ke yin tattaki mako-mako da ayarin El-Rufai da ya kai ziyara a unguwar Bakin Ruwa a ranar Alhamis da yamma.
- NAJERIYA A YAU: Shin Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zai Shafi Na Gwamnoni?
- Gwamnatin Jigawa ta ware N22bn don aikin tituna
Jami’an tsaron sun bude wuta ne bayan wasu mabiya Shi’a da ke yin tattaki a lokacin da Gwamna El-Rufai ke wuce su sun fara yi wa ayarin ihu.
Ana cikin haka ne wasu matasa suka fara jifar ayarin gwamnan, lamarin da ya kai ga jami’an tsaro sun mayar da martani ta hanyar bude wuta.
Lamarin dai ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali, a yayin da shaidu suka tabbatar da rasuwar mutum hudu sakamakon arangamar.
Wani wanda aka kashe dan uwansa mai suna Yusha’u a rikicin ya ce dan uwan nasa ba dan Shi’a ba ne, direba ne, amma harsashin jami’an tsaron ya yi ajalinsa.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin kuma wasu mutane da ake zargi sun shiga hannu.