Mutum uku ne aka samu labarin mutuwarsu yayin da aka fafata kazamin rikici tsakanin ’yan sanda da masu tuka babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep a kan titin Command na Jihar Legas.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, rikicin ya fara ne lokacin da wani dan sanda mai bai wa ababen hawa hannu ya soka wa wani mai keke napep wuka a kirjinsa saboda ya ki ba shi Naira 100 da ya bukaci ya ba shi.
Bayanai sun ce hakan ne ya fusata sauran masu tuka keke napep din don haka sai suka bi dan sandan a guje amma ya tsere.
Daga nan ne kuma gungun masu keke napep din suka dauki gawar abokin aikinsu zuwa ofishin ’yan sanda na Meira suka ajiye ta.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa masu tuka keke napep din sun gudanar da zanga-zanga ne kan mutuwar dan uwan nasu a lokacin da suka kai hari ofishin ’yan sandan suka wurga kwalabe da duwatsu.
Gungun masu zanga-zangar sun yi kokarin kona ofishin ’yan sandan ne amma an tarwatsa su da harsasai da hayaki mai sa hawaye.
Wani mazaunin unguwar ya bayyana wa jaridar cewa harsashi ya samu wani mai facin taya da ke bakin titi inda ya mutu nan take.
Haka kuma, ya ce ’yan sanda sun ci gaba da harbi da sa hayaki mai sa hawaye inda mutum uku suka rasa ransu.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Legas ta bayyana cewa kwamishinan ’yan sanda a Jihar, Hakeem Odumosu ya aika da jami’ai don tabbatar da tsaro a unguwar.