Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce hare-haren masu dauke da makamai sun kashe mutane 645 a jihar cikin watanni shida daga watan Janairu zuwa Yuni wannan shekara ta 2022.
Hakan na kunshe ne cikin wani rahoton tsaro kan tashe tashen hankula da gwamnatin jihar ta fitar ranar Juma’a.
- Ba na garkuwa da mutane sai dai kawai na kashe su —Aleiro
- Ranar Laraba za a yi wa mai wakar Najeriya Jaga-Jaga dashen koda
Rahoton ya bayyana cewa, an kashe adadin wadannan mutane ne a hare-haren ta’addanci da fadan kabilanci da kuma na ‘yan fashin daji.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, a sanarwar da ya fitar ya ce kusan kashi daya bisa uku na wadanda aka kashe (234) an kashe su ne a Kudancin Kaduna.
“A cikin watanni shida na farkon shekarar 2022, mutane 645 ne suka rasa rayukansu a irin wannan yanayi a fadin jihar; 234 daga cikin wadannan sun faru ne a yankin Kudancin Kaduna,” in ji Mista Aruwan a taron gabatar da rahotannin zaman lafiya a tsakanin addinai.