An kashe wasu mayaƙan ƙungiyar ISWAP masu tayar da ƙayar baya a Afirka ta Yamma yayin wata arangama da ’yan Boko Haram a gabar Tafkin Chadi.
An dai yi fafatawar ce da mayaƙan Boko Haram ɓangaren Bakoura Buduma wanda ake yi wa laƙabi da Abou Umaymah.
Bayanai sun ce rikicin da ya kai ga artabun ya faru ne a tsibirin Kukiri da Lelewa da ke gabar Tafkin Chadi a Jamhuriyar Nijar.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Zagazola Makama, ƙwararre kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa an soma karon-battar ne a Yammacin ranar Alhamis, 11 ga Afrilun 2024.
Majiyar ta ce Abou Umaima ya jagoranci mayaƙan da suka dira a sansanin Lelewa da na Gadira a Bosso da ke yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar.
Ta ce mayaƙan sun ƙaddamar da farmaki a sansanin inda suka kashe mayaƙan na ISWAP da dama.
Sai dai rahoton na Zagazola ya ce kawo yanzu ba a gano haƙiƙanin alƙaluman mayaƙan ISWAP da aka kashe ba.