Al’ummar yankin Ngoshe a Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun shiga zullumi bayan ƙungiyar Boko Haram ta fille kan wasu mutum huɗu da ta yi garkuwa da su a yankin.
Bayan Boko Haram ta saki bidiyon fille kan mutanen — maza biyu da mata biyu — al’ummar Ngoshe sun shaida mana cewa waɗanda aka kashen suna daga cikin mutane bakwai, maza biyu da mata biyar da mayaƙan ƙungiyar suka yi awon gaba da su a yankin a makon da ya gabata.
A cikin bidiyon an ji wani shugaban ƙungiyar yana cewa sun yi wa mutanen haka ne saboda suna taimakawa wajen kai hare-hare da kashe mayaƙan ƙungiyar.
Bidiyon da wakilinmu ya samu ranar Laraba ya nuna mayaƙan Boko Haram suna holen mutane a wani wuri mai tsaunuka, wanda al’ummar Ngoshe suka tabbatar masa cewa yankin Gwoza ne.
- HOTUNA: Yadda aka kama ɓarawo bayan ya fasa gida ya kwashe kayan ciki
- NAJERIYA A YAU: Faduwar Tanka A Jigawa: “Mun Kasa Cin Abinci Tun Da Abin Ya Faru”
Wani mazaunin garin Ngoshe ya shaida wa wakilinmu cewa yawancinsu sun girgiza da ganin irin kisan rashin imani da aka yi wa ’yan uwan nasu.
“Tun da ake Boko Haram ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, wanda hakan ke nuna munin abin, musamman ganin yadda a baya-bayan nan ake ta kashe manoma da ba su ji ba, ba su gani ba.
“Wannan shi ne mafi muni abin da muka gani a tarihin Boko Haram a nan yankin kuma ya kamata cikin gaggawa Gwamnatin Tarayya ta sani.
A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram sun tsananta hare-hare tare da kashe manoma da sace musu ɗanyen amfanin gona a yankunan Ngoshe da Kirawa da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza.
A makon juya ne dai Sanata Ali Mohammed Ndume mai wakiltar Kudancin Jihar Borno ya koka da cewa ba a ba wa sojoji wadatatun kayan aiki da makamai domin yaƙar ’yan ta’adda.