✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ceto mutane 38 a hannun Boko Haram a Borno

Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa sun ceto mutane 38 da ƙungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a yankin Tafkin Chadi.

Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa sun ceto mutane 38 da ƙungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a yankin Tafkin Chadi.

Dakarun sun kuma lalata wata cibiyar sufurin mayaƙan ƙungiyar a yayin aikin a yankunan Kukawa da Baga da ke Jihar Borno.

Kakakin rundunar, Kanar Olaniyi Osoba, ya ce an ceto mutanen ne bayan sojojin sun yi arba da mayaƙan Boko Haram da ke safarar su.

“Mayaƙan tsarewa suka yi suka bar mutanen da sojoji suka ceto,  maza huɗu da mata mata takwas da kuma ƙananan yara 24,” in ji Kanar Osoba.

Ya ce mayaƙan na Boko Haram suna ƙoƙarin kai mutanen wani wuri ne daga maɓoyar ƙungiyar da ke Dogon Chikwu, wanda yanzu sojoji suka addaba da luguden wuta.

Kanar Osoba ya ƙara da cewa sojojin sun bi sawun mayaƙan ƙungiyar da suka tsere da nufin kamo su.

Ya ce a yankin Gubio kuma, sojoji sun kama gungun masu yi wa Boko Haram safarar kayayyaki da motoci uku ɗauke da kayan abinci da magunguna da tufafi da saura abubuwa, a hanyarsu ta zuwa sansanin ’yan ta’addan.